19 Yuni 2021 - 19:18
Zabebben Shugaban Kasar Iran Ya Ce Zai Bada Himma Wajen Warware Matsalolin Mutanen Kasar

Zabebben shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi ya bayyana cewa zai yi duk iya kokarinsa don kyautata rayuwa da kuma warware matsalolin da mutanen kasar suke fama da su.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Iran Press (IP) ya nakalto Sayyid Ra’isi ya na fadar haka jim kadan bayan an bayyana sakamakon zaben shugaban kasa wadanda aka gudanar a jiya Jumma’a.

Sayyid Ra’isi ya kara da cewa zai yi aiki tare da majalisar dokokin kasar, da kuma kwararru a dukkan fannoni, don ganin an kafa gwamnati wacce za ta sanya mutanen kasar Iran cikin farinciki da fata a ko wani lokaci.

342/